Aikin ceto PDP na Saraki ya fara samun tsaiko

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tuni dai kwamitin Sanata Bukola Saraki da jam’iyyar PDP ta kafa domin farfaɗo da jam’iyyar ya fara fuskantar barazanar da ka iya kawo cikas ga ayyukan ta.

Taron da ƙungiyar gwamnonin PDP da sauran masu ruwa da tsaki suka yi a Abuja a daren ranar Lahadin da ta gabata, sun yanke shawarar baiwa Saraki da tsofaffin gwamnoni da masu riƙe da madafun iko ikon gyara raunin jam’iyyar PDP gabanin zaɓukan 2027, da taka birki wajen sauya sheƙa, da tabbatar da taron kwamitin zartaswa na ƙasa a ranar 27 ga watan Mayu, ba tare da tada ƙayar baya ba, da kuma sauya salon jam’iyyar.

Sai dai wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na ƙorafin cewa ayyuka da furucin da wasu ‘yan jam’iyyar ke yi ba zai taimaka wa jam’iyyar PDP ta warware matsalolinta da dama ba.

Majiyar jam’iyyar ta bayyana barazanar da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas na jam’iyyar suka yi a baya-bayan nan na ficewa daga jam’iyyar idan har jam’iyyar PDP ta ci gaba da hana ɗan takarar shiyyar neman muaamin sakataren ƙasa, Sunday Ude-Okoye, ya karɓi muƙamin a matsayin wanda zai maye gurbin Sanata Samuel Anyanwu.

Majiyar ta bayyana sunan gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah a matsayin shugaban masu tayar da ƙayar baya, inda ta yi zargin cewa hakan wata hujja ce ga ƙungiyar ta sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Baya ga haka, ‘ya’yan jam’iyyar PDP da abin ya shafa na fargabar cewa ci gaba da rikicin ofishin sakatariyar ƙasa na iya haifar da asara ta fuskar fasaha a yayin da jam’iyyar ke shirin gudanar da zaɓen da za a yi a ranar 21 ga watan Fabrairun 2026 a ƙananan hukumomi shida na babban birnin tarayya.

A kodayaushe PDP na yin nasara a babban birnin tarayya Abuja amma yanzu tana fuskantar babbar barazana daga APC.

Mbah, tare da gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal; Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang; tsohon gwamnan Bayelsa Seriake Dickson; tsohon gwamnan Gombe Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan Abia Okezie Ikpeazu, mambobi ne a kwamitin Saraki.

Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Enugu, Cif Ugochukwu Agballah, wanda ya karɓi sama da mutane 150 da suka sauya sheƙa daga jam’iyyar LP da PDP a cikin wata ɗaya da ya gabata, ya sha alwashin hana Gwamna Mbah tsallakewa zuwa jam’iyyar APC, yana mai zargin cewa tuni jam’iyyar APC ta fi cancanta da karɓar ragamar mulkin jihar a shekarar 2027.

Baya ga raɗe-raɗin da ake ta yaɗawa game da yiwuwar sauya sheƙar Gwamna Mbah da aaalla ɗaya daga cikin gwamnonin Arewa daga jam’iyyar PDP, gamayyar jam’iyyar da ke rikici da juna na haɗa ƙarfi da ƙarfe da masu ruwa da tsaki a harkar shari’a a shirye-shiryen tunkarar rikicin da ka iya barazana ga manufofin kwamitin Saraki.

By ukarofi