NAHCON ta gudanar da addu’a ta musamman ga Tinubu a Madina

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar malamai da NAHCON ta zaɓa daga jihohin Kudu maso Yamma sun gudanar da addu’a ta musamman a Madina domin neman taimakon Allah ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabannin Najeriya. Sheikh Afini Yusuf AbduIbari, shugaban majalisar limamai da Alfas ta Etiosa a jihar Legas, ya bayyana cewa manufar addu’ar ita ce nuna godiya da kuma neman kariyar Allah ga shugabanni domin ci gaba da yaƙi da rashin tsaro da kuma sauya fasalin ƙasar.

Sheikh AbduIbari ya bayyana cewa Shugaba Tinubu tun bayan hawansa mulki yana aiki tuƙuru ba tare da gajiyawa ba, hakan yasa suke da buƙatar ci gaba da masa addu’a. Ya ƙara da cewa malamai daga jihohin Legas, Osun da Oyo ne suka hallara a Madina domin gudanar da wannan ibada. Haka kuma ya yabawa NAHCON kan yadda suka gudanar da aikin jigilar alhazai cikin tsari, musamman ɓangaren karɓar baƙi, masauki da abinci.

A cewarsa, fiye da alhazai dubu arba’in sun isa Madina kuma an ci gaba da wayar da kai ga alhazai kan ma’anar aikin Hajji.

Malamai sun gudanar da ziyara a wuraren ibada masu tsarki, ciki har da Masallacin Annabi(SAW) inda suka gudanar da addu’ar. Sheikh Ridwan Mustapha Sunusi ya ƙara da cewa addu’ar na da nufin taimakawa gwamnati wajen ciyar da ƙasa gaba, tare da gargaɗin alhazai da su kiyaye dokokin Saudiyya da kuma na addini da na Najeriya.

By ukarofi