Kurkukun Abuja: An sallami ƴan Shi’a 56, an kama 33 da laifi – Hukuma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mai shari’a Husseini Baba Yusuf na Babbar Kotun Tarayya ya sallami fursunoni guda 56 daga gidajen yari biyu a ƙarƙashin Hukumar kula da Gidajen Yari ta ƙasa (NCoS) reshen Birnin Tarayya Abuja.

Kakakin NCos na Abuja, Samson Duza ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Alhamis, inda ya ce 30 daga ciki an tsare su ne a kurkukun Kuje yayin da aka tsare sauran a kurkukun Suleja.

A yayin wani hukunci kuma, Alkali Belgore ya jagoranci sauraron ƙarar wasu mambobin ƙungiyar Shi’a (IMN) guda 58 da aka tsare da gidan yarin Kuje, inda aka sallami 25 daga ciki har da mace ɗaya.

Ya ce, guda 33 kuma an tabbatar da laifukan da ake tuhumar su da aikatawa inda aka cigaba da tsare su.

A yayin haka ne Alķalin ya biya wa ɗaya daga cikin waɗanda aka wanke kuɗin sufuri da biyan diyyar N100,000 ga wani bisa kyautatawarsa.

Kwantirolan NCoS na Abuja, Olatunbosun Ajibogun ya yaba wa alķalin bisa hukuncin nasa da ziyarar kurkukun, yana mai cewa za su cigaba da tabbatar yin adalci ga kowane fursuna.

By Babaji