Su Shekarau na son a yi kama-kama a sauke Tinubu a 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƴan demokraďiyya ta Arewacin Nijeriya, wato The League of Northern Democrats (LND) ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ta yanke shawarar goyon bayan haɗakar ƴan ɓangaren adawa domin sauke Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta ƙunshi sanannun jagororin ƴan siyasa, malamai da ƴan kasuwa daga Arewacin Nijeriya, wadda ta bayyana matsayarta a yayin wani zama da ta gudanar, ranar Alhamis.

A sanarwar da fitar, kamar yadda ɗaya daga cikin mambobinta, Umar Ardo ya karanto, LND ta ce aƙalla mutane 147 ne suka halarci taron cimma matsayar goyon bayan haɗakar a ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark.

Ta ce, za su bada cikakken goyon baya wajen samar da wata jam’iyya ko kuma haɗewa da ɗaya daga cikin waɗanda ake da su.

LND ta kuma yanke cewa, za ta gana da baki ɗaya gwamnoni 19 na Arewacin Nijeriya akan halin tsaro da tattalin arziƙi a shiyyar.

“Za mu wayar da kan ƴan arewa wajen matsa wa gwamnati musamman jagorancin majalisar dokoki wajen tsayuwa akan aiki da hukuncen-hukuncen da kundin dokar da suka yi rantsuwa a kai ta zo da su”, inji sanarwar.

By Babaji