Sanatocin Katsina sun amince Dikko Raɗɗa ya zarce

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Zaɓaɓɓun sanatoci da ‘yan majalisar tarayya a Jihar Katsina ƙarƙashin jami’yya mai mulki ta APC sun sanar da amincewa da kuma tabbatar da gwamnan jihar Umar Dikko Raɗɗa a matsayin ɗan takarar jami’yyar a zaɓen 2027.

Sanatocin ta bakin ɗaya daga cikinsu, Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua a cikin wani bidiyo da suka fitar, ya ce sun gamsu da salon mulkin gwamnan, wanda hakan ya sa suka amince da ci gabansa a matsayin ɗan takararsu.

Sanatan ya ce sun yaba da ƙoƙarin gwamnan wajen ci gaban jihar, musamman saboda cika alƙawuran da ya yi wa al’ummar jihar kamar tsaro da ilimi da noma wanda ya sa suka gamsu da shi.

Sanatocin sun kuma yi kira ga al’ummar jihar ta Katsina da su goyi bayansu, su kuma ƙara bai wa gwamnan goyon baya a tsare tsarensa da ke da nufin kawo ci gaba a jihar.

By ukarofi