Daga SALIHU MAKERA a Bauchi
Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da yin jabun takin zamani inda ta lalata haramtacciyar masana’antarsu.
Wata sanarwa da ta fito daga kakakin rundunar SP Ahmed Mohammed Wakili ta ce a ranar 10 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, jami’an sashen binciken sirri na rundunar, bayan samun bayanan sirri, sun kama wani mai suna Muhammad Abubakar da ake zargi da sarrafa sinadaran kashe ciyawa masu haɗari a gidansa da ke zaune a Unguwar Magaji Kaatas a Bauchi, a cikin kasuwa yana ɗauke da buhu shida na taki da ake zargin an gurɓata su da kuma kwalabe 46 na sinadarin kashe ciyawa da ake zargi an gurɓata.
Ahmed Wakili ya ce binciken da aka gudanar a gidansa bayan samun takardar yin bincike ya gano abubuwa masu nasaba da laifin da suka haɗa da katan 38 na sinadarin kashe ciyawa iri-iri da buhuna taki 14 samfurin NPK.
Sauran su ne buhu 9 na takin Indorama da jarka ɗaya mara komai da cokula biyar da murhun gawayi da kwalayen robobi da buhuna ɗauke da garin “Ztars” da “Lambda powder.”
Ya ce, wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da bayyana Abubakar Umar, mazaunin yankin a matsayin abokin harƙallarsa.
Har wa yau, a ranar 14 ga Mayu 2025, rundunar ta ga wani shagon da ake zargi da sarrafawa da sayar da jabun mallakin Anas Abubakar, mai shekara 32, da ke kan titin Gombe a garin Bauchi inda aka kama shi da buhu 44 da rabi na jabun taki.
Sanarwar ta ce, Anas Abubakar ya ce ya sayi gurɓataccen takin ne daga wani mai suna Abdulrahman Muhammad, mai shekara 24, da ke zaune a Unguwar Bakaro a garin Bauchi. Sai dai ya musanta cewa yana sayar da jabun takin, amma ya amince cewa yana sayar da kayan da ake amfani da su, irin su sinadarin kaolin da ake zargin ana haɗawa da taki don gurɓata shi.
Ya ce yana samo kayan ne daga Ziya’u Bala, mai shekara 27, a Unguwar Guɗum Hausawa a Bauchi. Sanarwar ta ce an kama Ziya’u, inda ya jagoranci jami’anta zuwa ƙauyen Natsira a hanyar Kangere, inda aka gano wani katafaren wurin da ake sarrafa jabun takin.
A wurin, an gano buhun jabun taki 44 da buhu100 na garin kaolin da aka gauraya.
Sanarwar ta ƙara da cewa an gano wasu masana’antu biyu da a ke yin jabun taki da ake zargi na wani mai suna Sama’ila Abdullahi, mai shekara 34, a ƙauyen Natsira da Mujahid Abdullahi, mai shekara 32, a ƙauyen Kangere.
‘Yan sandan sun lalata haramtattun masana’antun uku, tare da ƙwace dukkan na’urorin da ake amfani da su.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da sa ƙafar wando ɗaya da masu aikata ba daidai ba, kuma duk wanda aka kama zai gurfana a gaban kotu don amsa tuhuma.
