‘
Daga UMAR GARBA a Katsina
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kashe jami’an tsaron al’umma na Katsina, wato ‘Katsina Security Community Watch Corps’ guda biyar.
Mummunan harin ya yi sanadin mutuwar Kwamandan jami’an tsaron na C-Watch, Malam Sanusi, wanda ke da alhakin kula da tsaro a yankunan Kusada, Kankia, da wasu sassan Charanci. Haka kuma, an kashe wasu jami’ansa guda huɗu yayin da suke tafiya cikin wata motar Hilux don kai ɗauki a ƙauyen Maharba dake ƙaramar hukumar Matazu bayan samun bayanan sirri dake nuni ce wa ‘yan bindingar na shirin kai hari.
Shaidun gani da ido sun ce harin ya afku ne a lokacin da jami’an tsaro suka amsa kiran da aka yi musu na cewa akwai ɓarayin daji a yankin.
Maharan waɗanda adadinsu ya kai kusan 20 kuma kan babura, sun yi wa jami’an tsaron kwanton ɓauna ne a kusa da wani gaɓar kogi da ke kusa da ƙauyen. Sun ɓoye a cikin bishiyoyi inda daga nan ne suka buɗe wuta tare da ƙona motar sintiri ta jami’an tsaron bayan sun harbe dukkan mutanen biyar da ke ciki.
Saboda haka ne gwamna Raɗɗa ya yi gaggawar jagorantar wata tawaga ta jami’an tsaro zuwa wurin da aka kai harin domin tantance adadin ɓarna tare da ɗaukar matakan da suka dace.
Tawagar ta haɗa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Dr Nasiru Muazu; Kwamishinan ’yan sandan jihar; daraktan hukumar kula da ayyukan jami’an tsaro na DSS da kuma shugaban ma’aikatan gwamna, Alhaji Abdulkadir Nasir, da dai sauransu.
Tawagar ta samu tarba daga shugaban ƙaramar hukumar Matazu, Alhaji Shamsudeen Sayaya.
Gwamna Raɗɗa ya duba wurin da lamarin ya faru, sannan ya ziyarci wuraren dake da wuyar isa wurin domin tattaunawa da mutanen yankin da kuma fahimtar ƙalubalen tsaro da ke addabar yankin.
Da yake jawabi bayan ziyarar, gwamna Raɗɗa ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamna Raɗɗa ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, inda ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamatan, ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa ‘yan uwansu haƙurin jure rashin.
