Da Ɗumi-Ɗumi: Alonso ya gaji Ancelotti a matsayin kocin Real Madrid

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta tabbatar da Xabi Alonso a matsayin sabon kociyanta.

Tsohon ɗan wasan na Sifaniya da Real Madrid ya dawo Saniago Bernabéu ne a matsayin babban mai horarwa bisa yarjejeniyar kwantaragin shekara uku.

A ranar 1 ga watan Yuni, 2025 ne wa’adin kwantaragin zai fara aiki, inda zai ƙare ranar 30 ga Yunin 2028.

Naďin Alonso zai fara aiki ne a nan take inda zai fara da jagorantar ƙungiyar a wasannin ƙungiyoyin ƙasashen duniya, wato Club World Cup, wanda za a fara a ranar 14 ga watan Yuni a Amurka.

Alonso, mai shekaru 43, ya dawo Madrid ne bayan rawar-gani da ya taka a ƙungiyar Bayer Leverkusen ta ƙasar Jamus, inda ya lashe gasar Bundesliga na kakar 2023/2024 ba tare da tashin nasara ko guda ba, da kuma kofin DFB-Pokal.

By Babaji