
Daga BELLO A. BABAJI
Wani zama na musamman da ya haɗa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar LP da Rotimi Amaechi da sauransu ya samu tsaiko a lokacin da wasu deliget daga Jihar Jigawa suka hargitsa shi.
Ana gudanar da taron haɗakar ne a Otal ɗin Abuja Continenta Hotel dake Birnin Tarayya, wanda ƙungiyar mashawarta kan harkar siyasa ta ƙasa reshen Arewa ta shirya.
An samu matsala ne a lokacin da aka kasa cimma matsaya game da batun wakilci daga Jihar Jigawa a lokacin da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya umarci wani da ya yi magana madadin jihar.
Lamarin da ya sa wasu dandazon masu zaɓe suka kutsa cikin fushi da hana shi magana, inda daga nan ne jami’an tsaro suka shigo tare da dawo da aminci a ďakin taron.
Baya ga haka ne aka zaɓi Mustapha Lamiɗo, ɗan tsohon gwamnan jihar, Sule Lamiɗo da wani da su yi magana a madadin jihar.
