‘Yan Sanda a Katsina sun kama wata matar aure da zargin kashe kishiyarta

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mijin matar Nasiru Yusuf ya kai rahoton ga ofishin ‘yan sanda a Sabon Garin Daura bayan da dawowa gida daga kasuwa yaga uwargidan nasa cikin jini.

Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar wa manema labarai da afkuwar lamarin.

Mijin nasu da suke zaune a bayan makarantar firamare na unguwar Dadi ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya shiga gidansa bayan ya dawo daga kasuwa sai yaga uwargidan sa kwance jina jina.

Koda ‘yan sanda suka garzaya da ta asibitin gwamnatin tarayya da ke garin Daura kafin su isa ta rasu.

Yan sandan sun sami nasarar kama Rabi’atu Labaran yar shekara 23 da haihuwa kuma abokiyar zaman marigayiya zainab bisa zargin aikata kisan kai

Amaryar ta tabbatar wa ‘yan sanda cewa ita ta daɓa wa kishiyar na ta wuƙa bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninsu.

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa a halin yanzu ‘yan sanda na cigaba da bincike “da zaran su kammala bincike zasu tura wadda a ke zargin aikata laifin kisan kan a gaban kuliya.

Kwamishinan yan sanda CP Bello Shehu ya yi kira da iyali da su guji rikice rikicen cikin gida wanda babu abinda zai haifar in banda da ruguza zuriya.

By ukarofi