Rikicin PDP ya yi ƙamari bayan Wike ya janye daga sulhu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rikicin jam’iyyar PDP ya ɗumi a ranar Lahadi a yayin da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fice daga yarjejeniyar sulhun da aka cimma a tsakanin ƴaƴanta.

Wike ya zargi Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde kan zama sababi na matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar, inda ya ce gwamnan ba ya bin ka’idodin yarjejeniyar da aka gindaya.

A sanarwar da ya fitar, Wike ya zargi jagororin jam’iyyar waɗanda suka haɗa da Gwamnan Enugu, Peter Mbah da butulci da rashin gaskiya gami da karya ka’idodin sulhu.

Ministan na Abuja, wanda tsohon gwamnan Ribas ne kuma ɗaya daga cikin ƙungiyar gwamnoni biyar na G5, ya kuma zargi Makinde da yi wa shirin sulhun zagon-ƙasa.

Ya ƙara da cewa, tun bayan zaɓen 2023 jam’iyyar ta shiga mawuyacin hali a sakamakon rashin gaskiya da cin amana daga jiga-jigan ƴaƴanta, lamarin da aka yi ta ƙoƙarin shawo kai amma aka gagara har zuwa yanzu.

Don haka ne Wike ya ķudiri aniyar ficewa daga tawagar sulhun duba da cewa ba a shirya daina ababen da suke haifar wa jam’iyyar matsaloli ba, kamar yadda ya bayyana.

By Babaji