Bayan da wani matashi ɗan shekara 33 ɗan ƙasar Japan mai suna Honkon ya yi tarin kuɗi na tsawon shekaru 10 don sayen motar da yake buri na wata sabuwar mota ƙkrar Ferrari 458 Spider, sai ya zauna yana kallon yadda motar take ƙonewa cikin sa’a ɗaya da tuƙa ta a karon farko.
Kafofin sada zumunta na ƙasar Japan sun yi sharhi game da rahoton baƙin ciki na Honkon, matashin da ya kasance mai shirya waƙoƙi, wanda ya kashe maƙudan kuɗi game da mafarkin sayan motarsa ta Ferrari, sai dai ya kalle ta tana ci da wuta a ranar da ya tuƙa ta a karon farko.
ɗan shekara 33 kwanan nan ya dauki hankalin mabiya manhajar ɗ (Twitter) don yaɗa labarin kan yadda zai ji daɗin gaskata mafarkin mallakar Ferrari a ’yan mintuna kaɗan kawai ta kama da wuta yayin da yake tuƙi a kan babbar titin Shuto a Tokyo, Laraba, 16 ga Afrilu.
A bayyane yake, an kawo masa zaɓinsa Spider 458 ne kawai, kuma yana cikin motar kan gwaji tare da shi lokacin da ya lura da fitar wani farin hayaƙi.
Da farko ya ɗauka hayakin daga motar da ke kusa da tasa motar yake fita, amma yayin da motar ta yi gaba, sai ga shi hayakin yana fitowa daga cikin motar Ferrari.
Don haka sai kawai Honkon ya janye, ya fita daga cikin motar, ya kira hukumar kashe gobara.
Ya kwashe mintuna 20 yana kallon burinsa ta ƙone kusan gaba ɗaya.
“Ina tsammanin ni kaɗai ne mutum a Japan da ya taba fuskantar irin wannan matsala,” Honkon ya rubuta a shafin ɗ, tare da taken hoton motar da ke ƙonewa.
“Na kashe yen miliyan 43 kwatankwacin (Naira miliyan ɗari 4 da miliyan 92 dubu ɗari 283 da 620), kuma abin da na samu shi ne wannan hoton.”
Rundunar ’yan sandan birnin Tokyo ta sanar da cewa, babu alamun karo a jikin motar Honkon ta Ferrari, amma ana ci gaba da gudanar da bincike.
An yi imanin cewa gobarar ta tashi ne a cikin injin motar, amma har yanzu ba a san dalilin ba.
Yayin da a fili yake matashin ya yi baƙin cikin rashin motarsa, Honkon ya shaida wa mabiyansa cewa ya yi farin ciki da ya rayu, domin yana tsoron cewa motar za ta iya fashewa yana ciki.
