Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Shugaban ƙaramar hukumar Gombe kuma shugaban majalisar ƙananan hukumomin Jihar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya kai ziyara ga yara masu fama da ciwon sikila a wasu asibitoci a birnin Gombe, don bikin ranar yara na bana ta wata siga ta musamman.
A yayin ziyarar, Barista Sani Haruna ya bayyana cewa an shirya wannan ziyara don jajantawa yaran tare da nuna soyayya da ƙauna gare su, yana mai cewa yaran na da matuƙar muhimmanci a ginin al’umma.
Ya yi kira ga iyaye su mai da hankali kan lafiyar ‘ya’yansu ta hanyar bin shawarwarin likitoci da samar da magunguna da abinci mai gina jiki.
Haka nan, ya miƙa tallafi na kuɗi ga iyayen domin rage musu nauyin jinyar yaran.
Shugaban ya kuma yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da su haɗa kai da gwamnati wajen samar da kayan jinya da ƙarin tallafi ga marasa lafiya masu fama da wannan larura a Gombe da ma Najeriya baki ɗaya.
A ƙarshe, ya yi kira ga al’umma su wayar da kan jama’a kan cutar sikila, musamman muhimmancin gwajin jini kafin aure domin rage yawaitar cutar a cikin al’umma.
