Yara mata 104,000 a Katsina suka amfana da kayan karatu da rubutu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya sanar da haka da yake jawabi a wajan taron tunawa da ranar yara ta duniya a filin wasa na Muhammadu Dikko.

Ya ce wannan adadin yara mata sun fito ne daga makarantun sakandare 255.

Gwamnan ya bayyana cewa yaran sun kuma amfana da tallafin kuɗi kowannen su, duk a manufar gwamnati na rage yawan yaran da basa zuwa makaranta.

Ta wajen fanin kiwon lafiya kuwa gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da cewa yara miliyan 2.2 aka yiwa allurar riga-kafin cutar ƙyanda.

“Haka kuma mun sanya Naira miliyan 200 a haɗaka da hukumar Unicef domin magance matsalar yara masu fama da cutar ƙarancin abinci mai gina jiki”inji Dikko Raɗɗa.

Domin taimaka wa yaran wajen koyon sana’o’in hannu gwamnatin jihar ta horas da yara 200 sana’o’i daban daban domin dogaro da kai, gwamnan yace.

Mun biya kuɗin kudin jarabawar kammala makarantar sakandare ta NECO da WAEC,NABTEB da NBAIS domin samun ingantaccen ilimi a jihar inji malam Dikko Raɗɗa.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana wannan rana mai muhimmanci da za ta tuna mana irin mahimmanci da yara ke da shi,”haka kuma ba wai yara manyan gobe bane kawai a’a kadara ce a cikin al’ummar mu a cewar sa”ya ce.

Yaran da suka fito daga makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da dama suka halarci taron inda suka gudanar da faretin girmamawa a gaban gwamna Dikko Raɗɗa.

By ukarofi