Daga USMAN KAROFI
Kotun Tarayya da ke zaune a Kano ta yanke wa shahararriyar yar Tik Tok Murja Ibrahim Kunya, wadda aka fi sani da Murja Kunya, hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bisa laifin cin zarafin Naira.
Alƙalin kotun, mai shari’a Simone Amobeda ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2025, bayan Murja ta amsa laifin ta na taka da wulaƙanta takardun Naira.
Hukuncin ya biyo bayan bincike mai zurfi da hukumar EFCC ta gudanar a kan lamarin, wanda daga baya ya kai ga kama ta da kuma gurfanar da ita a kotu.
