Wike ya bijire wa umarnin Tinubu, ya ƙi buɗe Hedikwatar PDP da aka rufe a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Kula da Birnin Tarayya (FCTA) ƙarƙashin jagorancin Ministan Abuja, Nyesom Wike ba ta buɗe Hedikwatar Jam’iyyar PDP ba duk da umarnin Shugaba Bola Tinubu.

A ranar Litinin ne jami’an FCTA suka fara rufe filaye da gine-ginen da ba a biya musu kuɗaɗen hayar ƙasa ba wato ‘ground rent’.

A watan Maris, 2025 ne Wike ya ƙwace filaye 4,794 a birnin tarayyar.

Akan haka ne Shugaba Tinubu ya umarci a dakatar da ɗaukar matakin inda ya nemi a ba su wa’adin kwanaki 14 na su biya kuɗaɗen bashin hayar da ake bin su, kamar yadda Daraktan kula da filaye, Chijioke Nwankwoeze ya tabbatar a wata takarda.

Ya ce, kuɗaɗen sun kai na tsawon shekaru daga 10 zuwa 42, lamarin da ya sa aka ƙwace su.

An ga yadda wasu ma’aikatan jam’iyyar ke zaune a wajen ofishin yayin da wasu kuma suka fake a wasu wurare.

By Babaji