Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kamar yadda gwamnatin Kano ƙarƙashin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bai wa ilimi muhimmanci ta hanyar ware kaso 30 cikin 100 na kasafin kuɗi a shekararsa ta farko ta mulki, kuma ya ware kashi 31 cikin 100 a shekararsa ta biyu ta mulkin Kano wanda haka ne ta sa aka samu bunƙasar ilimi a faɗin jihar Kano, ake gina makarantu da ajijuwa da kuma gyaran makarantu da ma sauran fannonin cigaban rayuwa al’ummar Kano da gwamnan Kano ke yi a kodayaushe.
Hakan ta sa ƙaramar hukumar Ungogo ke koyi da Gwamnan Kano kamar dai yadda Shugaban ƙaramar Hukumar, Hon. Tijjani Amiru ya bayyana a lokacin da ya jagoranci hukumar ilimin ta ƙaramar hukumar a gidan gwamnatin Kano wajen karɓar dubban litattafan karatu da rubutu da gwamnan ya raba wa ƙananan hukumomi 44 na Kano.
Har ila yau ya ƙara da cewa shi a matsayinsa na shugaban ƙaramar hukumar Ungogo kullum koyi yake yi da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo da kuma jagoran Kwankwasiyya wajen kawowa Kano cigaba ta kowanne fanni.
“To haka abin yake a ƙaramar hukumar Ungogo wanda yanzu haka an samu bunƙasar ilimi a ƙaramar hukumar bisa jagorancin gwamnan Kano da kuma mu shugabanni a matakin hukuma.”
A ƙarshe ya yi kira ga malaman makaranta da iyaye da sauran al’ummar Ungogo a kan su bai wa gwamnati Kano da ta ƙaramar hukumar haɗin kai wajen bunƙasa ilimi da tarbiyya da kuma sauran fannonin cigaba kamar lafiya, noma, kasuwanci, tsaftar muhalli da dai sauran abin da zai bunƙasa rayuwar al’umma a kodayaushe.
