Mun gamsu da wakilcin da Hassan Husaini ke yi wa Nasarawa – Bomboy

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Jigo a tsarin Kwankwasiyya a jihar Kano a ƙaramar Hukumar Nasarawa, Hon. Muhammad Adamu da aka fi sani da Bomboy, ya ce a matsayinsu na ‘yan ƙaramar hukumar da suke tare da ɗan majalisar su na tarayyar sun godewa Allah da irin zaɓi da jagoran Kwankwasiyya na ƙasa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi musu na tsayar musu da Hon. Hassan Shehu Husaini da aka yi suka zaɓe shi a matsayin wakilinsu a majalisar tarayya.

Ya bayyana haka ne ga manema labarai ya ce domin zuwan sa majalisar tarayya ya zo da ƙudurce-ƙudurce da suka shafi bunƙasa cigaban al’ummar yankin idan aka yi duba da ɓangaren harkar ilimi wanda shine ƙashin bayan tafiyar madugunsu na Kwankwasiyya da Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ya yi abubuwa da yawa da bunƙasa lafiya da kyautata zamantakewa da ayyukan bunƙasa rayuwa.

Hon. Muhammad Adamu Bomboy ya yi nuni da cewa daga ƙudurce ƙudurce da ɗan majalisar nasu Hon. Hassan Shehu Husaini ya kawo a zuwansa majalisa cikin kusan shekaru biyu yana mutuƙar yin hidima akan abinda ya shafi cigaban al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa da jihar Kano gaba ɗaya.

Ya ce irin ayyuka da ya yi sun haɗa da na haɓaka Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da sama musu cibiya ta kula da ciwon zuciya sannan ya kai ƙudiri na haɓaka ɓangaren masana’antu a jihar Kano.

Ya ƙara da cewa a irin koyi da yake da shi na tsarin tafiyarsu ta Kwankwasiyya yana bai wa ilimi kulawa sosai ya ɗauki nauyin karatun yara ƙanana marasa gata tun daga makarantar reno har firamare har gaba ya kuma ɗauki nauyin jarabawar ɗalibai tun daga NECO da WEAC da JAMB.

Ya ƙara da cewa sannan ya na ɗaukar nauyin karatun ɗalibai a manyan makarantu daban-daban a ciki da wajen Kano da gina ajujuwa da asibitoci da gudanar da tituna a mazaɓu da dama da sanya fitilun masu hasken rana da samawa matasa ayyukan yi da tallafawa matasa da jari ya tallafawa mutane da dama da ababen hawa yan siyasa da sauran al’umma a fannoni da dama.

Hon. Muhammad Adamu Bomboy ya ce suna godiya ga Allah da ya basu wakili da a cikin shekaru biyu ya bijiro da ayyukan da har sai da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ya zo ƙaddamar da wasu daga ayyukansa ya yaba masa ya nemi sauran yan majalisu ma su yi koyi da shi.

By ukarofi