Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ɗaya daga cikin maniyyata aikin Hajjin bana daga jihar Filato mai suna Hajiya Zainab ta mayar wa da wani ɗan ƙasar Rasha kuɗinsa da ta tsinta a birnin Makka na ƙasar Saudiyya, har kimanin Naira miliyan takwas da dubu 200.
Rahotanni sun nuna matar ta tsinci guzirin maniyyacin ne a Masallacin Harami na Makka a ranar Talata.
Ta tsinci kuɗin ne da yawansu ya kai Dala dubu biyar, kimanin miliyan takwas da dubu 200 a Naira, idan aka canza a kan farashin N1,648 a kan kowacce Dala ɗaya.
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) da kuma Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Filato, Hon. Dayyabu Dauda duk sun tabbatar da faruwar lamarin.
“Ta nuna halin dattaku, gaskiya da riƙon amana ta hanyar mayar da Dala dubu biyar ɗin da ta tsinta a masallacin harami ga mai su. Haƙiƙa ta nuna halin nagarta da tausayi,” inji Hon Dayyabu.
A wani labarin kuma, hukumar ta NAHCON ta nuna rashin jin dadinta da yadda ɗaya daga cikin maniyyatan jihar Zamfara ta haihu a Madina a makon nan.
Hukumar ta ce ta yi mamakinn yadda matar ta tsallake duk gwaje-gwajen da ake yi a kokarin hana masu juna biyun da suka kusa haihuwa tafiya.
Sai dai ta ce za ta yi cikakken bincike domin ta gano a ina aka samu matsalar.
