‘Yan Nijeriya miliyan 20 ne ke da taɓin hankali – WHO

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya, WHO,  ta fitar ya ce ‘yan Nijeriya miliyan 20, daidai da kashi 20 cikin 100 na al’ummar ƙasar, na fama da matsalar taɓin-hankali.

Dr Azubike Aliche, Sakataren Kwamitin Amintattu na Cibiyar Kula da Lafiyar ƙwaƙwalwa ta Najeriya-Amurka (NAIMH) ne ya bayyana haka a wani shirin horo kan lafiyar kwakwalwa da GAP Action da cibiyar su ka shirya a Owerri a jiya Talata.

Ya bayyana cewa “lamarin mai tayar da hankali ne” game da ciwon damuwa da ‘yan Nijeriya ke fama da shi, wanda ya ce, ya kasance mafi girma a duniya kuma ya yi kira da a yi ƙoƙari matuƙa don canza yanayin.

“Rahotanni da ake samu sun nuna cewa kashi 10 cikin 100 na masu fama da taɓin hankali ne kawai ke samun kulawa a Nijeriya kuma dole ne a canza wannan yanayi,” inji shi.

By ukarofi