Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruƙ Umar-Faruƙ, ya ce, sare bishiyu ya fi aikata ta’addanci muni, saboda yana haifar da babbar barazana ga muhalli.
Sarkin Daura ya bayyana haka ne a garin Daura ranar Juma’a, a lokacin da Saleh Abubakar, Darakta Janar na Hukumar Kula da Tsirrai ta ƙasa, NAGGW, ya ziyarce shi.
A cewar Sarkin, Majalisar Masarautar ta ɗauki matakin yanke bishiyu a yankin a matsayin babban laifi, domin yana iya haifar da illa ga al’umma.
Uban gidan sarautar ya ce, da daɗewa Majalisar Masarautar ta yanke hukuncin cewa yankan bishiyoyi daidai yake da kashe ɗan Adam.
A cewarsa, saboda muhimmancin dashen bishiyu, masarautar ta bayar da hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da laifin sare itatuwa.
Ya ƙara da cewa, galibin ƙalubalen muhallin da ke fuskantar yankuna da dama, na faruwa ne saboda sare itatuwa.
Umar-Faruƙ ya ce, majalisar masarautar Daura ita ce ta farko a faɗin ƙasar nan musamman ta fannin dashen itatuwa.
“Majalisar Masarautar ta shirya tsaf don tallafa wa hukumar wajen rabon irin bishiyoyi, domin hakan zai rage rashin aikin yi, da kuma rashin tsaro,” inji shi.
Sarkin ya kuma yi alƙawarin ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin dashen itatuwa a yankin, inda ya buƙaci jama’a da su dasa da kuma kula da bishiyu domin yaƙar sare itatuwa da kare muhalli.
Ya buƙaci hukumar da ta magance saran itatuwa a dazuzzuka da kuma illar da ke tattare da muhalli, wanda hakan zai iya haifar da shiga hamada da kuma sauyin yanayi.
Tun da farko, babban daraktan hukumar ya ce sun kai ziyarar ne domin neman goyon bayan sarkin domin yaƙi da sare bishiyoyi.
A cewar Abubakar, wannan lamari yana shafar filayen noma, yana kashe dabbobin gida, don haka akwai buƙatar mazauna yankin su rungumi ɗabi’ar dashen itatuwa, domin kyautata muhalli.
Ya ce an daɗe ana tafka ta’asa, amma abin ya wuce yadda ake tsammani a ‘yan kwanakin nan.
“Saboda haka, idan aka hana, za mu shaida amfanin sa a lokacin damina, kuma hakan zai baiwa manoma damar girbi da bunƙasa tattalin arziki.
“A cikin ‘yan kwanakin nan, muna fuskantar zafi mai yawa saɓanin da, dasa bishiyoyi ne kawai zai iya hana wannan lamarin,” inji shi.
A cewarsa, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Daura, ya ji daɗin ganin ɗimbin filaye da dashen itatuwa.
Ya shaida wa Sarkin cewa hukumar za ta ziyarci jihohin Arewa 11 da take gudanar da ayyukanta kuma Katsina na ɗaya daga cikinsu, yayin da Daura na daga cikin muhimman wuraren da ya kamata a ziyarta.
“Hukumar tana da shirin rarraba a faɗin jihohinmu da muke aiki, kimanin iri na dabino na Saudiyya miliyan 5, waɗanda za su iya girma kuma a yi amfani da su cikin shekaru huɗu,” inji Abubakar.
A cewarsa, idan aka yi shuka da girbi bayan shekaru huɗu, Nijeriya na iya samun sama da Naira Biliyan 300 daga cikinta, domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Hukumar tana aiki a jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa, Kebbi, Kano, Zamfara, Sakkwato, Yobe, da Katsina.
