Shukar Buhari muke girba a wannan mulkin

Spread the love

Daga MUSBAHU BAFFA 

Wato tarihin ƙasar nan ba zai taɓa cika ba har sai an ambaci Buhari a matsayin mutumin da ya fi kowani mai mulki rashin iya mulki da kuma cutar al’ummar ƙasar nan.

A ƙarƙashin mulkin Buhari NNPC da CBN suka zamanto mallakar wasu tsirarun mutane da sai yadda suke so ne zai faru a ƙasar nan. Su ne kuma mahangar tattalin arziƙin ƙasar nan. 

A ƙarƙashin mulkin Buhari hukumar EFCC ta bankaɗo kwagilolin fiye da Naira Tiriliyan 2 wanda an fitar da kuɗaɗen, ba a aiwatar da ayyukan ba. Babu kuma wanda aka nuna da yatsa ballantana a tsangwama.

A ƙarƙashin mulkin Buhari harkar tsaro ta koma kasuwanci mafi riba tsakanin jami’an tsaron ƙasar nan.

Tsakanin al’ummar ƙasar nan da Buhari sai dai mu yi fatan Allah ya masa irin riƙon da ya yi wa ƙasar nan, don alfarmar Annabi Muhammadu (SAW).

Musbahu Baffa ɗan siya sa ne kuma mai sharhi kan al’amurran yau da kullum musamman na siyasa. Ya rubuto ne daga Abuja

By ukarofi