Daga ISAH ABDULLAHI DANKANE
Haɗin kan shuwagabannin jihar Zamfara tun daga gwamna mai ci a yanzu da ƙaramin ministan tsaron Nijeriya wanda yake ɗan asalin jihar Zamfara ne da tsofaffin gwamnoni da sanatocinmu da ‘yan majalisarmu na tarayyar da ‘yan majalisun jiha tare da malamman addini da ‘yan kasuwa da sarakuna da duk wasu masu faɗa-a-ji a Zamfara shi ne hanyar samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar Zamfara.
Al’ummar jihar Zamfara matsayinku na mutane masu ilmi, waɗanda addinin musulunci ya yi tasiri a kansu kuma mutane masu riƙo da gaskiya da mayar da alheri da alheri. Ina mai amfani da wannan dama a matsayina na mai koyo wanda bai ko kai darajar almajiri a cikinku ba; ina mai bai wa junanmu shawara cikin mutuntawa da girmamawa ba tare da bayyana ra’ayi irin na siyasa ba.
Ni ina ganin duk mutumin da yake kishin jihar Zamfara da gaske ba kishi irin na siyasa ba, to akwai inda ya kamata ya ba da tashi gudummawa game da sha’anin tsaro a wannan jiha ba ta hanyar sukar Gwamnati ba, domin kuwa har abada cin zarafin gwamnati ba zai taɓa zama maslaha ga sha’anin tsaron wannan jiha ba.
Al’ummar jihar Zamfara, wallahi matsalar tsaron da wannan jiha ke fama da shi, Jarabawa ce daga gurin Allah (SWT) abin ya wuce a yi wasa da hankali. Mu daina yaudarar kanmu da abinda ba wannan ba, mu cire siyasa mu kalli abin da idon basira.
Shi fa kowane mutum a duniyar nan ɗan tara ne bai cika goma ba, kuma kowane ɗan Adam ajizi ne. Mu yi wa gwamnati adalci; a cikin gwamnati akwai sanatoci da ‘yan majalisu waɗanda suke da manyan kwamitoci. Idan har masoyanku ne ina suke ne? Shin na ce ina suke ne? Wane irin hoɓɓasa suka yi game da sha’anin tsaron yankunanmu?
Al’ummar jihar Zamfara, wallahi Allah (SWT) adili ne kuma ba ya zalunci sannan bai yarda mu yi zalunci ba. A jihar Zamfara akwai mutanen da suke so su jingina wannan matsala ga Jami’an tsaro ko kuma gwamnati, ya kamata su fito su bayyana wa duniya mutanen dake da alhakin kashe al’ummar wannan jiha, tun da ba su yarda da Allah ne ya kawo wannan Jarabawar ba, ko sai lokacin siyasa idan sun sake buƙatar kuri’unku?
Al’ummar jihar Zamfara, menene ribar ƙarya da ƙage ko sharri a kan matsalar tsaron wannan jiha? Wannan matsala ta kowa ce, duk wanda yake kishin jihar Zamfara ni ina ganin ya kamata komi rashin ƙarfinsa akwai inda amfaninsa yake, sai ya ba da tasa gudunmawa gwargwado, amma ba mutum ya fake da matsalar tsaro ba yana sukar gwamnati ba, bayan mutanen ƙauyuka a wannan jiha suna cikin musibar mahara. Bayyana wa duniya gaskiyar halin da wannan jiha ta ke ciki shi ne zai sa bayin Allah daga ko’ina a duniya su taimaka mana da addu’oi ba ta hanyar yin rubuta a kafafen sadarwa da manufar matsalar tsaro don cin zarafin gwamnati ba.
Al’ummar jihar Zamfara, matsalar tsaron nan, wallahi sai an cire siyasa da banbancin ra’ayi, sannan a yi wa kowa adalci, a tunkari matsalar tsaron gadan-gadan da gaske, kuma al’umma kowa ya gyara tsakaninsa da Ubangijinsa a kuma bi shawarwarin dattawa masana tsaro, sai kuma a yi addu’oi a masallatai da makarantun Islamiyya, idan ta kama a ɗauki malaman addinin musulunci su tafi ƙasa mai tsarki domin roƙa wa jihar Zamfara mafita sai a yi hakan.
’yan’uwana Zamfarawa, Ina godiya ƙwarai da mutuntawarku a gare ni. Allah (SWT) Ka kawo wa al’ummar jihar Zamfara ɗauki irin naKa, Allah ka kuɓutar da al’ummar wannan jiha, dan ƙima da mutuncin Annabi Muhammad (SAW).
Danƙane, matashi ne ɗan gwagwarmaya da ke fafutukar kare haƙƙoƙin matasa. Shi ne shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers na Jihar Zamfara. Ya rubuto daga Jihar Zamfara
