Tinubu ya ƙarfafa sojoji da kayan aiki don bunƙasa tsaro a ruwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da jiragen ruwa guda uku na sojojin ruwa, wato NNS SHERE, NNS FARO da NNS IKOGOSI, sai kuma helikwafta uku ƙirar AW109 Trekker masu lambobi kamar haka; 501, 502 da 503.

A lokacin da ya ke magana yayin ƙaddamarwar a Legas, ranar Asabar, Tinubu ya ce sun ƙara jiragen sintirin ne domin tabbatar da bai wa yankunan ruwan Nijeriya tsaro yadda ya dace.

Tinubu, wanda Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya wakilce shi, ya ce yankunan tekunan Nijeriya ginshiƙi ne na nasarori ga harkokin tattali.

Sannan, ya bayyana cewa sama da tsawon shekaru 69, rundunar sojojin ruwa ta tsayu wajen ganin ta bai wa ɓangaren kariya da inganta shi.

Ya kuma ce, sababbin jiragen ruwan da helkwaftocin za su taimaka wajen yaƙi da satar jiragen ruwa, satar mai, su (kamun kifi) ta haramtattun hanyoyi da wasu manyan laifuka da ake gudanarwa a ruwa.

Haka kuma, Shugaban ƙasar ya tabbatar wa sojojin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da fifita buƙatunsu domin samun nasara a harkar tattalin arziƙin ƙasa.

Daga ƙarshe, ya yaba wa Shugaban rundunar, Vice Admiral Emmanuel Ogalla bisa jagorancinsa wajen tabbatar da rundunar da samu kayan aiki na zamani da inganta ɓangarorinta da dama, wanda hakan ya taimaka wajen dawo da martabarta.

By Babaji