
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain ta yi nasarar lashe kofin gasar zakarun Nahiyar Turai, wato UEFA Champions League na kakar 2024/2025.
Hakan ya biyo bayan lallasa Inter Milan ta ƙasar Italiya da ta yi da ci 5 da 0 a wasan ƙarshe.
Wannan shi ne karo na farko da PSG ta taɓa lashe gasar tun bayan kafuwarta a watan Agustan shekarar 1970.


