DAGA MUKHTAR YAKUBU
Amir Iliyasu yana ɗaya daga cikin fitattun jarumai da suke haskawa a cikin shirin ‘Dadin Kowa’, na tashar Arewa 25 wanda yake fitowa a matsy ɗan daba wato Garzali.
Duk da cewa tsohon ɗan fim ne da ya kasance mai shirya finafinai a masana’antar finafinai ta Kannywood wanda ya shirya finafinai da dama irin su ‘Jarin Ibo’ da ‘Asusun Ibro’ waɗanda suka shahara a wancan lokacin musamman waƙar ‘baba sai mini mai ross a sa a dakin aure na’ ta cikin fim ɗin ‘Jarin Ibo’.
Domin jin ko wanene Amir Iliyasu maiross. Wakilinmu a Kano Mukhtar Yakubu, ya tattauna da shi don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.
MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar da kanka.
MAIROSS: Amir Iliyasu maiross, ko Garzali a cikin shirin ‘Dadin Kowa’ kuma ni an haife ni a Unguwar Danya cikin garin Wudil da ke cikin Jihar Kano a shekarar 1983 kuma abin da ya shafi rayuwata, na yi karatun firamare da sakandare duk a cikin garin Wudil, kuma bayan na kammala na tafi Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi na yi karatuna na NCE, kuma bayan na gama, na bayar da gudunmawa ta a ɓangaren koyarwa a makarantu, haka nan da yake ɗalibin makarantar islamiyya ne ina koyarwa a Makarantar Islamiyya har yanzu.
Ko a wanne lokaci ne ka fara harkar fim?
To harkar fim na fara ta ne tun a 2003, kuma na fara fim ne a matsayin furodusa wanda na fara da fim ɗin ‘Asusun Ibro’, kuma ba zan manta ba a lokacin mahaifina ne ya fara bani kuɗin da na yi jarin fim ɗin, shi ne ya ara mini dubu goma na zo na haɗa da ɗan abin da nake da shi. Kuma daga nan Allah ya sanya wa abin albarka na samu fim ɗin ‘Asusun Ibro’ ya samu karɓuwar da duk wani mai kallon fim a lokacin ya san fim ɗin ‘Asusun Ibro’. Wannan ya sa na ci gaba da shiryawa, inda na yi fim guda biyu, daga nan dai sai harka ta ci gaba na yi J’arin Ibo’ ‘Makari’ ‘Uwar Manya’, ‘Wa Ya Fi Wani’, ‘Tuggu’ Bara’atu”, ‘Zuciya Na So’, ‘Gaba da Gaban Ta’, ‘Ya Halatta’. Da sauran su.
A yanzu an fi sanin ka a matsayin jarumi. Ko ya aka yi ka rikiɗe daga furodusa zuwa jarumi?
To ko a can baya daman ina fitowa a matsayin jarumi, amma ba sosai ba. To sai daga baya na ga idan muka je waje, jaruman kawai ake gani ba a ganin mu. To sai na ga ni ma ina buƙatar na zama jarumin da za a rinƙa gani na. Kuma cikin ikon Allah sai na samu shiga a cikin shirin ‘ɗadin Kowa’ na tashar Arewa 25 wanda nake fitowa a matsayin Garzali. Wanda hakan ya ba ni damar fitowa a cikin finafinai da dama a yanzu a matsayin jarumi ba furodusa ba kamar yadda aka sanni a baya ba, kuma jama’a sun sanni sosai a matsayin jarumi a yanzu , wanda hakan ya ba ni damar kulla alaƙa da manyan mutane a ciki da wajen ƙasar nan.
Kuma Alhamdulillah ta dalilin harkar fim na samu damar yin mu’amala da mutane. Kuma na samu gogayya ta ilimi da ƙwarewa, don na samu takardun shaida wadda hukumomi da kuma ƙungiyoyi kwararru suka ba mu horo a kan harkar fim da sauran kasuwancin zamani.
Kuma Alhamdulillah, harkar fim ta ba ni damar yin tafiye-tafiye inda na je ƙasashen Nijar, Kamaru da Ghana.
Ko ya kake kallon yadda harkar fim take a yanzu musamman kai da ka daɗe a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood?
To gaskiya ita harkar fim a yanzu ta zama ta zamani, domin a baya ana yin fim ne a kai shi kasuwa. A yanzu kuma harkar fim ta zama mai tafiya da zamani, don haka da su masu shirya fim ɗin, da jaruman kowa sai ya tafi da zamani. Ka ga a baya idan ka yi fim ɗin kasuwa za ka kai a saya a ba ka kuɗin ka. To yanzu kuma sai dai ka yi kasuwancin na zamani. Ko dai a manyan gidajen talbijin, ko kuma a Youtube, don haka idan mutum ya shirya fim dole sai ya yi daidai da irin wanda ake buƙata a yanzu. To kuma wannan ci gaba ne aka samu na zamani, kuma duk wanda zai yi harkar fim a yanzu, dole sai dai ya bi wannan tsarin. Hakan ce ta sa mutane da dama aka bar su a baya. To gaskiya ina tafiya ne da zamani don haka ban yarda an bar ni a baya ba. Ko a yanzu na ga wata sabuwar fasaha ta zo a cikin harkar mu. Zan yi ƙoƙarin na ga na samu ilimi a kan ta. Don duk wanda ka ga ya iya to koya ya yi, wannan ya sa ba zan yarda a bar ni a baya ba.
A yanzu wanne irin buri ka sa a gaba a game da harkar fim?
To buri na dai na ga na samu nasara a duk harkar da na saka a gaba. Alhamdulillah a baya lokacin da ina matsayin furodusa, sai da na samu damar zama cikin firodusushin da ake ya yi, to a yanzu da harkar ta juya na samu kaina a matsayin jarumi, ina fatan na samu ɗaukakar da ko’ina za a rinƙa kiran sunana.
Me ya fi burge ka a cikin harkar fim da ka daɗe ka na yi?
Babu abin da ya fi burge ni kamar haɗuwa da mutanen arziki, don kamar yadda na faɗa maka a baya wannan harkar ta haɗa ni da mutane da dama da muka yi harkar arziki, kuma suka zama abokan arziki a gare ni.
Alhamdulillah sai dai fatan Allah ya sa mu gama lafiya.
To Madalla mun gode.
Ni ma nagode sosai.
