Yadda Akpabio ya nemi na karɓo masa cin hanci daga ministoci – Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sanatar da aka dakatar daga Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi zargin cewa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya buƙaci da ta razana ministoci da jagororin hukumomi da nufin ya samu cin-hanci da wasu alfarma domin amfanin kansa.

A yayin hira da wata ƴar jarida kuma ƴar Nijeriya da ke zaune a Amurka, Adeola Fayehun, Natasha ta ce lallai akwai salon tursasawa a majalisar, tana bada misali da kasancewar ta shugabar kwamitin albarkatun cikin gida wanda aka yi yunƙurin amfani da shi wajen tatsar ma’aikatu da hukumomi ciki har da ministan man fetur da Gas da kuma Hukumar Ci-gaban Arziƙin Gida ta Ƙasa (NCDMB).

Ta ce, alaƙarta da Akpabio ta fara tsami ne a lokacin ya nemi ta ba shi rahoton halin da ake ciki game da buƙatun nasa, inda ta ce masa ta shirya takardun tsare-tsare akan aikin, lamarin da ya sa ya shashantar da rahoton nata.

Daga nan ne ta ce, ta fahimci abinda ya ke nufi da matakin da ake ciki na ta ba shi cin-hanci da karɓar manyan ayyuka da wasu ababe daga hukumomin.

Akan haka ne Natasha ta ce, ba za ta iya yin abinda ya ke nema daga gare ta ba, inda ta ce Akpabio ya yi ikirarin cewa matuƙar ba za ta iya razana ministocin ba, to ba ta cancanci zama shugabar kwamitin ba.

Ta ƙara da cewa, Akpabio ya fi mayar da hankali akan abinda zai samu ba wanda zai amfani ƙasa ba da al’umma ba.

Har’ilayau, Natasha ta kuma nesanta kanta daga zargin hannu a cewa ƴan majalisa sun yi kutsen wasu ayyuka a kasafin 2025.

Daga ƙarshe, ta jaddada zarginta akan Akpabio na batun cin-zarafi, inda ta ce tana neman damar da za ta gabatar da shi ne a gaban kotu ko tawagar bincike.

By Babaji