Da farko ina amfani da wannan kalma ce domin mu faɗakar da juna ta fuskar gano illar masu ɗabi’a ta tashi mu je.
kalmar tashi mu je daga jin ta za a fahimci ta tattaro yaudara da ƙarya tare da ba ta lokaci ga wanda duk a kai ma hakan.
Jama’a har kullum mu riƙa yi wa kawunan mu awo na adalci a madadin ga matsala a tattare da mu a gefe mu nai ma wasu kallon su ne ma su aikata laifuka.
Misalin tashi mu je, mutum ne ka na zaman ka zai zo ko kuma ya kirawo ka a waya yai ma ka albishir da wata samayya a zahiri wanda a ƙarshe idan tafiya tai nisa ka rasa inda wancen alkawarin ya ke.
A tsarin Musulumci an hane mu da yin karya. Haka an hane mu da yaudara wanda duka munanan ɗabi’u ne da su ka zamo jiki ga wasu a yau. Kar ka yi ma mutum alƙawari na karya kawai domin ka burge shi. A kullum mu zamo masu gaskiya tun daga zuci da a aikace. Mu guji yin karya ko neman suna kawai domin mu burge. Gaski ita ke tabbata.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa.07066434519/08080140820.
