Babbar Sallah: ‘Yan sanda sun jaddada hana hawan sallah a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da al’umma ke cigaba da gudanar da shirye-shiryen sallah a Kano, rundunar ƴan sandan jihar da haɗin-gwiwar hukumomin tsaro sun nanata haramta bukukuwan hawan sallah a jihar.

A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, rundunar ta ce ta ɗauki matakan da suka dace wajen tabbatar da zaman lafiya a yayin gudanar da hidindimun sallar tare da kira ga al’umma da su kasance masu kiyaye doka da oda da kuma ƙaurace wa duk wani abinda ka iya haddasa fitina.

Rundunar ta kuma tunatar da al’umma haramta hawan salla da ta yi a lokacin ƙaramar sallah a sakamakon samun bayanan sirri na barazanar tsaro ga zaman lafiyarsu.

Ta ce, har yanzu akwai barazanar tsaro a jihar, lamarin da ya sa ta ɗauki matakin cigaba da tafiya akan hukuncin a wannan karon.

Hakan ya biyo bayan shawarwari da masu-ruwa-da-tsaki kan harkokin tsaro da ta yi bisa la’akari da bayanan sirri da ke nuna cewa akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin amfani da bukukuwan hawan sallah wajen tada zaune-tsaye.

Daga cikin abubuwan da aka hana akwai Kilisa (tseren dawakai), tseren mota, tuƙin ganganci, mallaka ko bayyana makami ba bisa doka ba gami da ɗaukar abinda ka iya tsoratarwa ko zama abin zargi.

Kazalika, ta shawarci iyaye da su riƙa gargaɗin ƴaƴansu da na ƙasa da su akan bin doka sau da ƙafa tare da ƙaurace wa munanan ayyukan da ka iya jefa rayuwarsu cikin haɗari.

By Babaji