
Daga BELLO A. BABAJI
Babban masani a harkar likitanci kuma tsohon Ministan Ilimi da Fetur, Farfesa Jibril Aminu ya rasu.
Marigayin ya rasu ne bayan ya shafe shekaru 85 a duniya, inda ya riƙe manyan muƙamai a Nijeriya.
A ranar Alhamis ne farfesan ya rasu a Abuja bayan fama da wani rashin lafiya da ya ɗauki tsawon lokaci yana jinya a kai.
Haka kuma ya riƙe muƙamin jakadan Nijeriya ga Amurka a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2003.
Daga bisani ya zama Sanata a 2003 har zuwa 2011, inda ya wakilci mazaɓar Adamawa ta Tsakiya a majalisa.
