Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jihar Katsina ta samu guraben koyar da sana’o’i sama da 3,500 a ƙarƙashin sabon shirin gwamnatin tarayya na ilimin fasaha da koyar da sana’o’i ƙarƙashin shirin TVET.
Farfesa Idris Bugaje, babban sakatare na hukumar kula da ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE) ya bayyana haka a yayin da ya kai ziyara a cibiyar koyon sana’o’i a Katsina.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ita za ta ɗauki nauyin horon gaba ɗaya.
Bugaje ya cigaba da cewa bayan alawus na wata wata na Naira 22,500 na tsawon watanni shida ga masu samun horon za kuma su sami tallafin kuɗi Naira 180,000 da kayan fara sana’a.
“Bugu da ƙari, sanarwar waɗanda suka sami horon za su samu rance mai sauƙin kuɗin ruwa don tallafawa harkokin kasuwancin su,inji Bugaje.
Farfesa Bugaje ya bayyana canjin da aka samu daga takardar shaidar nazari,”horon dole ne ya kasance yana da alaƙa da masana’antu na gaske ,aiki na gaske da kuma rayuwa na gaske.
Shirin TVET mai taken “cigaban ƙwarewa da samar da makomar”zai gudana a cibiyoyin kasuwanci, cibiyoyin koyar sana’o’i.
Injiniya Kabir Ƙofar Soro shugaban Cibiyar koyar da sana’o’i a jihar ya bada tabbacin cewa cibiyar sa za ta fara wayar da kan matasa da dukkan ƙananan hukumomi da ke jihar kamar yadda gwamna Raɗɗa ya umarta.
