Shettima ya ƙaddamar da asibitin African Medical Centre of Excellence a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ƙaddamar da Asibitin African Medical Centre of Excellence (AMCE) a Abuja, wanda wani katafaren cibiyar kiwon lafiya ne da aka gina ta hannun Afreximbank tare da haďin-gwiwar Kings College Hospital London. Wannan cibiya babbar nasara ce ga lafiyar al’umma a Afirka wadda kuma ta ke zama alamar ci-gaba da ƙirƙire-ƙirƙire a fannin lafiya da aka gina a Nijeriya domin amfanin Nahiyar da duniya baki ɗaya.

Haka kuma Cibiyar tana da matsayi mai muhimmanci a Abuja Najeriya inda aka tanadar da ita domin bayar da kulawa ta musamman a fannonin cututtukan daji (cancer) jini (haematology) da cututtukan zuciya da jijiyoyi (cardiovascular) Haka kuma tana sahun gaba wajen binciken kimiyya da likitanci musamman a bangaren fasahar kwayoyin halitta (stem cell) magungunan nukiliya da na’urorin gano cututtuka.

An tsara cibiya don ta yi tasiri a faɗin nahiyar Afirka inda ake sa ran za ta kula da fiye da marasa lafiya 350000 a cikin shekaru biyar na farko Za kuma ta samar da fiye da ayyuka 3000 da kuma kasancewa da dakin gwajin kwayoyin halitta mafi girma a Afirka tare da na’urar Cyclotron na 18 MeV na farko a Yammacin Afirka wanda ke nuna matsayin ta a matsayin cibiyar bincike da magani mai zurfi.

Daya daga cikin manyan burin AMCE shi ne dakile yawon neman lafiya zuwa ƙetare (medical tourism) ta hanyar samar da ingantaccen kulawar lafiya a gida ga ’yan Afirka da kuma hana asarar ƙwararrun ma’aikatan lafiya ta hanyar jawo su su dawo gida daga ƙasashen waje Cibiyar na kuma da makarantar koyar da aikin jinya da likitanci domin horar da sabbin ƙwararru a fannin lafiya a Afirka

Wannan muhimmin mataki yana tafiya ne da hangen nesa na Sabuwar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ke nuna yadda Afirka ke kara samun ci-gaba da dogaro da kanta a fannin lafiya Kaddamar da AMCE na nuna irin ƙwarin gwiwa da ake samu cewa nahiyar Afirka na da ƙwarewar da za ta iya gina da kuma tafiyar da cibiyoyin kiwon lafiya masu daidaito da na duniya a cikin gida.

By Babaji