Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Jami’an Gwamnati Tarayya sun kai ziyara don duba aikin hanyar Burra zuwa Ningi a jihar Bauchi wanda Sanata Abdul Ningi ya nemo daga irin ayyukan da ake ba wakilai don aiwatarwa a yankunansu.
Jami’an da za su kula da fara gudanar da aikin hanyar Burra zuwa Ningi sun kai ziyara domin tattara bayanai da shirye-shiryen fara aikin hanyar.
Jami’an sun zo daga Birnin Tarayya Abuja tare da rakiyar Shugaban ƙaramar Hukumar Ningi, Hon. Nasiru Zakarai da mai tallafawa Sanata Abdul wato Alhaji Alhassan Ahmed da sauran ‘yan tawagar, inda suka bi hanyar tun daga Ningi har zuwa yadda ta kare a garin Burra.
Hanyar, wacce ke da tsawon kilomita 112, za a gyara ta ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Bankin Duniya.
Wannan gagarumin aiki ya samu ne sakamakon namijin kokarin da Sanata Abdul Ahmed Ningi ya yi wajen ganin an kawo sauyi ga rayuwar al’ummar yankin da suka jima suna shan wahala.
Wakilin mu ya rawaito cewa jami’an sun gudanar da wannan aikin rangadin na ranar Laraba.
Da yake jawabi bayan kammala duba hanyar a Fadar Hakimin Burra, shugaban karamar hukumar Ningi Hon. Nasiru Zakarai ya yaba da kokarin Sanata Abdul Ahmed Ningi, yana mai cewa al’ummar Ningi ba za su taba mantawa da wannan hidima da ya yi musu ba, saboda sun jima suna Shan wahala musamnan a lokacin damana. Don haka ya Yi fatar ganin karshen wahalar a daidai wannan lokacin.
Shima mai girma Hakimin Burra Alh Ya’u Shehu Abubakar, yace bayyi mamakin samo wannan aiki da Sanatan ya yi ba, saboda gogewar sa wajen kare muradun al’ummar da yake wakilta. Kuma sun jima suna kyautata masa zaton zai taimaka a share musu hawaye.
Don haka Hakimin ya gode wa Sanatan tare da alwashin bayar da haɗin kai ga ‘yan kwangilar da zarar sun zo domin fara aikin hanyar.
ɗan majalissar jiha mai wakiltar mazaɓar Burra, Hon Ibrahim Tanko Burra, shi ma ya gode wa Sanatan bisa wannan ƙoƙarin da ya yi don ceto su daga mawuyacin halin da suka shiga.
A yayin wannan ziyara, al’ummar Burra sun fito domin nuna godiya ga Sanata Abdul Ahmed Ningi bisa wannan ci gaba da suka dade suna jira. Kuma sun yi fatar Allah ya taimaka a samu fara aikin da kammala shi a kan lokaci.
