Noma ya fi cutuwa sakamakon rashin tsaro a Nijeriya – Ribaɗu

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Fannin noma ya fi samun cutuwa da koma-baya sakamakon rashin tsaron da ya addabi Nijeriya, kamar yadda Mai Ba Wa Shugaban ƙasar Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya yi iƙirari, inda ya ce kimanin ’yan Nijeriya miliyan 150 ne matsalar ta shafi rayuwarsu.

Ribaɗu, wanda ya bayyana hakan a yayin sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta ƙasa da Cibiyar Bunƙasa Noman Zamani, don haɓaka ayyukan noma a yankunan da ayyuakn ta’addanci ya addaba a Nijeriya, don inganta rayuwar al’ummomin da ke irin waɗannan gurare.

Ya ce, “rashin tsaro ne babbar matsalar da muke fuskanta a kowane fanni, amma fannin da ya fi samun nakasa shine na noma, domin ya shafi rayuwarmu gabaɗaya, saboda ’yan Nijeriya manoma ne. Ko dai kai manomi ne ko kuma ka fito daga zuri’ar manoma. Don haka ko ta wacce hanya ya shafe mu.

“Rashin tsaro ya birkita rayuwarmu. Za mu iya nasara ne kawai idan mu ka haɗa kawuna. Dole ne mu haɗa hannu wajen ganin mun dawo wa al’ummarmu rayuwarsu. Mutanenmu suna matuƙar buƙatar hakan.

“Ba na tsammanin akwai wata ƙasa a duniya da ta ke fuskantar ƙalubalen da mu ke fuskanta a yanzu, domin mu na da yawa sosai. Yawan mutanen da matsalar tsaro ta shafa ta yiwu sun kai miliyan 120 zuwa 150.”

Ya ci gaba da cewa, “mu kaɗai mu ka rage masu kuzari a yankin Sahel, saboda ƙoƙarin jami’an tsaro, amma mu na cikin matsanancin hali.”

A yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa, Ministan Kiwo na Nijeriya, Idi Muktar Maiha, ya yi kira ne da a koma gona kacokam, inda ya ce, “a maye gurbin motocib yaƙi da taraktocin noma… a maye gurbin bindigogi da na’urar tatsar madarar shanu a faɗin ƙasar.

“Idan har mutane su na da abin yi a gabansu, ba za a riƙa jan su a na kwaɗaita musu ta’addanci ba. Mu na so Nijeriya ta samu tambarin abin da mu ke so ta zama.”

By ukarofi