A ranar Juma’a ne Kotun Koli ta Amurka ta bai wa gwamnatin Shugaban ƙasa Donald Trump damar dakatar da kariyar doka da ke hana korar sama da ’yan gudun hijira 500,000 daga ƙasashen Cuba, Haiti, Nicaragua da Venezuela.
Wannan hukunci na nufin kusan mutane 532,000 da suka shiga Amurka ta hanyar shirin agaji na “parole” da tsohon shugaban ƙasa Joe Biden ya ƙirƙiro, za su iya fuskantar barazanar kora daga ƙasar.
Shirin “parole” na Biden ya bai wa ’yan gudun hijira daga waɗannan ƙasashe huɗu damar shiga Amurka na tsawon shekaru biyu, har zuwa mutum 30,000 a kowane wata. ƙasashen nan na fama da matsaloli na take haƙƙin ɗan adam, talauci da rikice-rikicen siyasa.
Sai dai gwamnatin Trump, wadda ke da tsattsauran ra’ayi kan harkokin shige da fice, ta ɗauki matakin jingine kariyar da shirin ke bayarwa, abin da ya janyo rikici a kotuna har ya kai gaban Kotun Koli a wannan watan.
Kotun, wadda yawancinta ke ƙarƙashin jagorancin masu ra’ayin mazan jiya (conservatives), ta amince da buƙatar gwamnatin Trump ta dakatar da hukuncin kotun ƙasa da ƙasa wanda ta hana korar, yayin da shari’ar ke ci gaba.
Hukuncin kotun bai bayyana dalilanta ba, kuma ba a sanya masa hannu ba. Sai dai manyan alƙalan kotun biyu, Ketanji Brown Jackson da Sonia Sotomayor, sun ƙi amincewa da hukuncin, inda suka gargaɗi cewa, wannan mataki zai haifar da “mummunan tasiri ga rayuwar dubban mutane.”
“Kotun ta yi sakaci a wannan yanke hukunci,” inji su a cikin takardar ƙin amincewa.
“Waɗanda abin ya shafa yanzu sun fuskanci zaɓin da babu mai daɗi: ko dai su bar Amurka su fuskanci haɗurran da ke ƙasashensu da kuma yuwuwar rabuwar iyali, ko kuma su zauna a nan su fuskanci kora da mummunan tasirinta.”
Kotunan kasa da kasa da suka hana gwamnatin cire kariyar sun ce gwamnati ta yi fassarar dokar shige da fice cikin kuskure da saɓani.
A lokacin yaƙin neman zaɓensa, Donald Trump ya yi alƙawarin korar miliyoyin baƙin haure da ke zaune ba bisa ƙa’ida ba a Amurka. Yana daga cikin matakan da ya ɗauka wajen nuna wannan ra’ayi ne, amfani da wata tsohuwar dokar lokacin yaki domin jigilar ɗaruruwan waɗanda ake zargi da zama ’yan kungiyar assha daga Venezuela zuwa gidan yari a El Salvador.
Yayin da wannan hukunci ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce, lauyoyin kare hakkin bil’adama da ƙungiyoyin rajin kare baƙin haure na cewa yana da matuƙar muhimmanci kotun ta duba wannan batu da cikakken adalci, ganin cewa rayuwar dubban mutane ce ke cikin hatsari.
