Wani mutum da ake zargi da damfara ya miƙa kansa ga EFCC 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani mutum da ake zargi da aikata damfara ta hanyar raba takardun ɗaukar aiki na bogi, mai suna Idris Adamu, ya miƙa  kansa  ga hukumar EFCC a ranar Litinin a jihar Gombe saboda zargin amfani da sunan wani da kuma karɓar kuɗi ta hanyar zamba.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Mista Oyewale ya ce an samu ɗan ƙaramin rikici a ofishin hukumar EFCC da ke shiyyar Gombe, lokacin da wannan mutum ya shigo cikin harabar ofishin ya kuma kai rahoto kansa kan laifukan da ake zarginsa da su.

Ya ce wanda ake zargin, Idris Adamu, ya bayyana cewa tsoron EFCC ne ya sa ya yanke shawarar miƙa kansa.

“Wanda ake zargin, Idris Adamu, ya shigo ofishin EFCC da misalin ƙarfe 1:00 na rana inda ya nemi ganawa da Muƙaddashin Daraktan Yanki, Kwamandan EFCC mai muƙamin DCE, Sa’ad Hanafi Sa’ad.

“Ya ce yana son ya bayyana wasu abubuwa da ya ɓoye game da laifukan da ya aikata a baya,” inji shi.

A cewar Oyewale, yayin da yake ofishin Daraktan, mutumin ya ce: “Na zo ne domin tuba daga zunubaina kuma in bayyana gaskiya ga EFCC.

“A baya na taɓa ƙarbar jimillar kuɗi har Naira miliyan tara ta asusun ajiyata daga hannun mutane daban-daban da nufin ba su guraben aiki a hukumomin gwamnatin tarayya, wanda ba gaskiya ba ne.

“Na sauya halina amma ina jin tsoron EFCC,” inji wanda ake zargin a cewar Oyewale.

Mista Oyewale ya ce muƙaddashin daraktan yankin, bayan sauraron wannan bayani, ya gode masa saboda nuna gaskiya da ya yi.

Ya ƙara da cewa Sa’ad ya bayar da umarnin a kai wanda ya miƙa kansa zuwa sashen bincike domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

By ukarofi