Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Makarantar Raudatul Jannah dake Rangaza ta ƙaramar Hukumar Ungogo a jihar Kano ta gudanar da walimar haddar ƙur’ani ga ɗalibai 45 na makarantar.
Taron da aka gudanar a ranar Lahadi ya samu halartar ɗinbin iyayen yara daga ciki da wajen ƙasar nan da shugabannin al’umma da malamai.
A yayin taron saukar mahaddatan an gabatar da kalandar makaranta inda mutane da dama suka bayar da gudummawa wajen ƙaddamar da kalandar.
Da yake ganawa da ‘yan jarida bayan kammala walimar Imam Muhammad Yakubu Daraktan na rukunin makarantun Raudatul Janna.
Ya ce walimar saukar shine na huɗu sun yi sauka ta farko a 2018 aka yaye yara takwas suka yi musaffa ta ƙur’ani sannan suka sake yaye 16 a karo na biyu sannan a karo na uku aka yaye 21 wannan na huɗu cikin wannan shekara ta 2025 an yaye yara 45 hafizai da suka yi musaffa ranar Laraba, Lahadi kuma aka yi bikin yaye su.
Ya ce nasara da suke samu ya taƙaita ne da yin abu da iklasin da jajircewa domin idan za ka yi abu kasa Allah a gaba zai baka nasara kamar lokacin da Imam Malik ya rubuta Muwaɗɗa Maliku ne sai aka ce masa ai an yi Muwaɗɗa da yawa sai ya ce a kawo ya duba da aka kawo sai ya ce zaku ga cewa wanda aka yi tsakani da Allah shine zai wanzu yanzu malamai da almajirai da yawa basu san akwai Muwaɗɗa ba bayan Muwaɗɗa Maliku saboda shi ya yi da iklasi ta wanzu.
Imam Muhammad Yaƙub ya ce farin cikin su shine na ganin yara ƙanana sun yi hadda kamar yadda suka yaye wata yarinya Hauwa’u ‘yar shekara shida da ta haɗa hadda a shekara ɗaya abin mamaki da wani yaro shi ma Al-Amin wanda ya gama haddarsa yana ɗan shekara bakwai ire-iren waɗannan abubuwa na ban mamaki na abin arziki ba ne ba akasin haka ba. Abinda ake yi yana bada mamaki yana yin fice babu shakka abin su godewa Allah ne.
Sannan ya yi kira ga iyayen yara da cewa duk haddar mutum da karatunsa yana buƙatar maraja’a da nazari ko mutumin da yake karatu a jami’a yana yin nazari yana karatu saboda haka idan ɗalibai suka dawo gida akwai buƙatar iyaye su sa ido akan wannan haddar yaro bai san muhimmanci da daraja da kimar abinda ya karanta ba amma kai mahaifi ka sani inka rabu da shi babu shakka haddar za ta lalace don haka yara su mayar da hankali iyaye su sa ido.
Ya ce kusan kaso 80 ciki 100 na ɗalibansu da suke yayewa sune ke jan sallar ƙiyamul laili a unguwanni da sukayi maƙotaka da su wannan na faranta musu rai amma ‘yan kaɗan ɗin da ba a basu kulawa ba sai aga babu haddar babu karatun wannan abin takaici ne.
Imam Muhammad Yaƙub ya yi kira ga gwamnati da muƙarrabanta akan su mayar da hankali akan ilimin addinin musulunci domin idan mutum tun yana ƙarami ya samu tarbiyya yasan haram da halak hukuma zata sami sauƙin aikata laifukan don yasan Allah ya hana shi kuma ya ginu a haka zai yi abinda Allah yake so amma rashin samun ilimi da tarbiyya shi yake wanzar da rashin aikin yi da rashin sana’a kuma yake kawo ta’addanci azo.ayi ta wahala kuma babu nasara Allah ya kiyaye.
