Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Alhazan Nijeriya, NAHCON ta bayyana cewa ‘yan ƙasar 2,717 ne suka kasa samun damar zuwa aikin Hajjin 2025 sakamakon biya a ƙurarren lokaci.
Cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yaɗa labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce duk da gazawar hukumarsu ta samun amincewa daga hukumomin Saudiyya na ƙara wa’adin rufe rajistar bizar ta samu biza 13,217 ga kamfanonin yawon buɗe ido daga cikin maniyyata 14,158 da suka yi wa rijista.
Hukumar ta NAHCON ta nemi afuwar mutanen da lamarin ya shafa, tana mai cewa zuwa Hajji kira ne na Ubangiji.
Tana mai bayar da shawara ga maniyyata da su riƙa biyan kuɗinsu a kan lokaci domin kauce wa.
Hukumomin Saudiyya ta ware wa Nijeriya kujeru 95,000 a aikin hajjin bana.
