Daga AISHA ASAS
Mawaƙiya Taylor Swift ta samu damar mallakar kundin waƙoƙinta na farko guda shida, bayan shekaru tana fafutukar hakkin mallakar ayyukanta. Wannan nasara ta zama wata babbar nasara ga masu fafutukar kare haƙƙoƙin fasaha.
Taylor ta ce, “Wannan nasara ta nuna cewa, bai kamata mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare haƙƙinmu.”
Lauya mai kare haƙƙin mawaƙa, Ms. Jennifer Collins, ta yi bayanin cewa, “Mallakar ayyuka abu ne mai muhimmanci wajen samun damar cin gajiyar ayyukan da aka ƙirƙira.”
