El-Rufa’i da Amaechi manyan maƙiyan ci gaban ƙasa ne, inji Yerima Shettima 

Spread the love

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna

Shugaban ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (AYCF), Alhaji Yerima Shettima, ya yi martani dangane da kalaman da tsohon Gwamnan jihar Kaduna El-Rufa’i da tsohon Minista Rotimi Amaechi suka yi a taron da suka yi a Abuja, inda ya bayyana kalaman nasu a matsayin soki burutsu.

Yerima Shettima ya ƙara da cewar a daidai lokacin da Nijeriya ke ƙoƙarin farfaɗowa daga matsalolin da suka addabe ta ɓangaren tsaro da tattalin arziki, abin takaici ne a samu irin waɗannan kalamai marasa kan gado na fita daga bakin waɗanda ake yi musu kallon manya.

Ya ƙara da cewar manyan maƙiyan cigaban ƙasa su ne waɗanda ke adawa ta son zuciya wadda za ta kawo rarrabuwa da koma baya a ƙasa.

Yerima ya yi kira da babbar murya ga matasan Nijeriya, da su kasance ‘yan ƙasa nagari masu nuna ƙaunar juna da haɗin kai a tsakaninsu, sannan su yi watsi da dukkanin wasu surutai na wasu manya, waɗanda buƙatar kansu suka sa a gaba ba rayuwar ‘yan ƙasa ba.

“Nijeriya za ta samu nasara ne da ciyar da al’ummarta gaba ta hanyar kishi da kyakkyawar siyasa, amma ba ta hanyar muguwar adawa ba.”

Shugaban matasan ya yi kira na ganin an samu adalci da daidaito a tsakanin ‘yan Nijeriya, domin samar da kyakkyawan yanayi a faɗin ƙasar.

By ukarofi