
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Nasarawa ta ƙaryata zargin cewa tana bai wa ƴan bindigar da ke kai hare-hare mafaka a wasu yankunan jihar, waɗanda suka yi sanadin rasa rayuka da dama da ɗaiɗaita ƙauyuka a Jihar Benuwai.
Mai taimaka wa Gwamna Abdullahi Sule kan harkokin al’umma, Mista Peter Ahemba ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Laraba.
Ya ƙaryata kalaman tsohon ɗan Majalisar Wakilai daga Benuwai, Mark Gbilah, wanda ya yi zargin cewa maharan ƙauyukan Benuwai suna samun wajen zama a Jihar Nasarawa.
Ya bayyana zargin tsohon ɗan majalisar, waɗanda ya yi su a yayin wata hira da gidan talabijin na AIT a matsayin zantuka marasa asali.
Mista Ahemba ya ƙara da cewa, yana da muhimmanci a faɗakar da al’umma game da kalaman mara tushe duba da yiwuwar su yi tasiri acikin al’umma wajen ruɗar da su.
Haka kuma, ya ce Gwamnatin Nasarawa tana aiki tuƙuru da jihohin maƙota musamman Benuwai wajen ganin an shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi al’umma.
Akan haka ne Gwamna A.A Sule ya kira taron gwamnonin jihohin Arewa ta Tsakiya wanda har da Gwamna Hyacinth Alia daga cikin mahalartansa, inda aka tattauna muhimman bututuwa kan lamuran tsaro.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga al’umma da su ƙaurace wa zargin tare da mayar da hankali akan ci-gaban haɗin kai a tsakaninsu.
