Wacce rana ce June 12 kuma me ya faru a cikinta?

Spread the love

A wannan ranar hawaye ya zuba, zuciyoyi sun raunata, an nakasa dubbai, an fusata da dama, an gajiyar da dayawa, wasu sun rasa rayukansu, a yayin da wasu kuma ke farin ciki da annushuwa.
June 12 rana ce ta tarihi, wacce ba za a taɓa mantawa da ita ba a Nijeriya. A wannan ranar ne ɗan takarar Social Democratic Party (SDP), wato Mashood Abiola ya fafata da ɗan takarar National Republican Convention (NRC) Bashir Tofa a babban zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1993. Mataimakin Abiola shi ne Baba Gana Kingibe, yayin da Sylvester Ugoh ya zama mataimakin Bashir Tofa. Duk da cewa masu sharhi na ganin zaɓen June 12 shi ne zaɓe mafi ingancin a tarihin ƙasar, amma sai gwamnatin mulkin soja ta wannan lokacin (Gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida) ta soke zaɓen bisa zargin maguɗi (a cewarta); wanda hakan ya haifar da gangarumar zanga-zangar da ta tilastawa Janar Babagidan sauƙa daga kan karagar mulki a ranar 26 ga August, 1993. Bayan ya sauƙa, aka kafa gwamnatin riƙon kwarya ƙarƙashin jagorancin Cif Earnest Shonekan, wanda daga baya Janar Sani Abacha ya hamɓarar da gwamnatin a wani juyin mulki da ake kira da ‘juyin mulkin falo’ a ranar 17 ga watan November, 1993. Dukan alamu sun nuna jam’iyyar SDP ta su Abiola ita ce kan gaba wajen lashe zaɓen da aka soke, wannan ya sa Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa a ranar 11 ga watan Yuli ɗin 1994 a Kihar Legas. Matakin da ya sa sabuwar gwamnatin Abacha ta zarge shi da cin amanar ƙasa, tare da kama shi ta tsare a ranar 23 ga July, 1994. An tsare Abiola na tsawon shekaru huɗu, inda wasu rahotanni sun ce ban da Alƙur’ani Mai girma da Littafi Mai Tsarki (Bibble) Abiola ba shi da wata hanyar samun bayanai.
An zargi mutane bakwai da taka muhimmiyar rawa wajen soke zaɓen June 12. Waɗannan mutane su ne:

1- Ibrahim Badamasi Babangida :- shugaban Najeriya wanda ya soke zaɓen da a kayi ittifakin shi ne zaɓe mafi tsafta a tarihin ƙasar.
2 – Sani Abacha :- yana cikin mambobin kwamitin mulkin soja (AFRC) da suka soke zaɓen. An yi ikirarin cewa ya taka muhimmiyar rawar gani wurin soke zaɓen tare da rufe wanda ake ganin shi ya lashe zaɓen a kurkuku.
3 – Arthur Nzeribe :- tsohon Sanatan da ya ba da babbar gudunmawa wurin soke zaɓen. Shi da Abimbola Davies suka kafa ‘Association for Better Nigeria’ ABN da ta nemi kotu ta dakatar da zaɓen wanda hakan ya bawa gwamnati damar soke zaɓen gaba ɗaya.
4 – Uche Chukwumerije :- yana cikin na hannun daman Abacha da suka riƙa goyon bayan kar a yi zaɓe a ƙasar.
5 – Walter Ofonagoro :- shi ma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka riƙa adawa da masu gwagwarmayar June 12. Mutane suna yi masa laƙabi da kakakin gwamnatin Abacha saboda yadda yake kare ƙudirorin gwamnatin.
6 – Lamidi Adedibu :- tsohon jigon siyasa a Jihar Ibadan. Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi ƙaurin suna don adawa da gwagwarmayar June 12. Saboda ya daɗe yana amfana da gwamnatin soja kuma yana bawa gwamnati bayanai kan ayyukan ƙungiyar ‘National Democratic Coalition’ da ke gwagwarmayar June 12.
7 – Abdulazeez Arisekola-Alao :- duk ɗan kasuwa mazaunin Ibadan ba zai taɓa manta abin da ya faru da Abdulazzez a Jami’ar Ibadan ba a watan November 1998. Ya tafi jami’ar tare da tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdulsalam Abubakar don hallartar bikin yaye ɗaliban jami’ar, amma ɗaliban jami’ar suka far masa suka ƙwace motocinsa suka ƙona su. Da kyar aka tseratar da shi a motar ‘yan sanda.

Dai kuma tsohon shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce ya ɗauki alhakin duk abubunwan da suka faru a lokacin mulkinsa ciki har da soke zaɓen June 12. Janar Babangida ya bayyana haka ne ranar Alhamis 20 February, 2025 a Abuja lokacin da yake jawabi wajen ƙaddamar da littafin tarihinsa da ya rubuta mai suna ‘A Journey in Sarvice’. Janar Babangida ya ce daga cikin abubuwan da yake danasanin yi a rayuwarsa har da soke zaɓen na 1993.
Shi kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce an soke zaben June 12 ne saboda bashin Naira bilyan 45 da Abiola yake bin gwamnatin tarayya. Sule Lamido ya alaƙanta soke zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar June 12 na shekarar 1993 da Marigayi Abiola ya lashe da bashin Naira bilyan 45 na kwangila da Abiola yake bin gwamnatin mulkin soja ta Marigayi Janar Murtala Mohammed. A cewar Sule Lamido, an ƙi biyan Abiola bashin bayan rasuwar Janar Murtala, kuma a lokacin da Abiola ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, sai aka soke shi saboda fargabar cewa idan aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa zai biyan kansa bashin, lamarin da ka iya durkusar da ƙasar a lokacin. Sule Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Talata 13 May, 2025 a Abuja a lokacin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘Being True to Myself’.
Wannan shi ne (a taƙaice) abin da ya faru a ranar June 12 ta shekarar 1993 wanda gwamnatin Najeriya ta keɓe ta domin gudanar da bikin ranar Dimukuraɗiyya a faɗin ƙasar.

Naku,
Mohammed Bala Garba, Maiduguri.
09042923950, 08069195272.

By ukarofi