Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Maiduguri
A daidai lokacin da ake tunawa da ranar Dimukuraɗiyya a Nijeriya, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum; tun da Asubah, ya ziyarci majinyata a asibitoci daban-daban a Maiduguri, inda ya fara da asibitin Ƙwararru ta jihar da misalin ƙarfe 5:00 na safiya, tare da baiwa majinyata tallafin kuɗi.
Wannan ya na ƙunshe a sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun Gwamnan, Malam Dauda Iliya, inda ya ƙara da cewa, gwamnan ya baiwa kowane majinyaci N50,000 dake jinya a asibitin.
Sa’ilin da yake tattaunawa da marasa lafiya a asibitocin, Gwamna Zulum ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na samar da ingantaccen tsarin kula da lafiyar al’ummar Kihar Borno.
Har ila yau kuma, gwamna Zulum ya ziyarci Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Maiduguri (UMTH), yayin da a nan ma ya tallafawa marasa lafiya da N50,000 kowanen su.
A hannu guda kuma, Gwamnan Zulum, zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan hanyoyi 20, waɗanda gwamnatinsa ta gina, a cikin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 2025.
Haka zalika kuma, zai ƙaddamar da aikin gina asibitoci biyu da kuma babban ɗakin taro na ƙasa da kasa a birnin Maiduguri da kuma a ƙaramar hukumar Jere.
Waɗannan asibitocin sun haɗa da asibitin ƙashi na Borno, dake Goni Kachallari, da babban asibitin Kaleri, a ƙaramar hukumar Jere.
A cikin Waɗannan shekaru shida a karagar mulki, Gwamna Zulum ya aiwatar da muhimman ayyuka sama da 1,000 a fannin ci gaban ilimi, kiwon lafiya, noma, hanyoyi, ruwa, muhalli, da makamantan su a faɗin Jihar Borno.
