Ranar Dimukraɗiyya: An tsaurara tsaro a Abuja yayin da aka fara zanga-zanga

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

An baza jami’an tsaro a Birnin Tarayya Abuja a yayin da wasu dandazon jama’a suka fara gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da halin matsin rayuwa da rashin tsaro da ake fama da su a ƙasar a birnin.

Hukumomin tsaro sun baza jami’an nasu ne a wurare mabanbanta a cikin birnin musamman inda ake sa ran ɓarkewar zanga-zanga.

Daga cikin wuraren akwai Eagle Square da Majalisar Dokoki, wato ‘National Assembly’ da wasu wuraren da masu zanga-zanga suka taru.

Lamarin ya yi daidai da Ranar Dimukraɗiyya a Nijeriya, inda wasu masu zanga-zanga suka fara tattaki daga yankin Apo tare da ganin su suna rera waƙe-waƙe da ɗaga alluna da ke ɗauke da rubutun da suke nuna halin ƙuncin rayuwa da al’umma suke fuskanta a ƙasar.

Haka kuma, an ga yadda jami’an tsaron suke cikin halin shirin ko-ta-kwana domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya acikin al’umma.

By Babaji