Lokacin ina sakandare JS2.
Nazo Bata Kasuwar Sabon Gari washe garin zaɓe faɗa ya ɓarke da Kyar na dawo gida a hiace. Aka saukeni a gidan zoo na falfala gida da gudu.
Lokacin babu waɗannan ƙayatattun gine-ginen na Zoo Road.
Ba Sahad Stores.
Ba ShopRite
Ba Bankuna.
Ba Oasis
Ba Sadaraki
Babu gidajen mai sai Total da Texaco na kusa da First Bank.
Babu gidan Ɗan Asabe
Babu Manyan Plazas ɗin Nan.
Titin ma ba a raba shi ba, hannu ɗaya ne kowa ya bi nasa ɓangaren.
Abinda yake na kaye kawai a Zoo Road Lokacin daga gidan Zoo ɗin sai gidan Buhari, sai Dangi Chemist, sai zoza gidan kifi, sai lambuna da wajen siyar da shuke shuke, sai wata rijiya daidai Sahad Stores ana Kiranta da SHA-DA-KOKO.
Sai kuma wani babban kanti ko shago dake kallon gidan ƙofar shiga gidan zoo ta biyu. Wato kantin Alhaji Aminu (Allah ya gafarta masa), sai Jamila Pharmacy dake kusa da gidan mai na Total.
Sai wajen sarki fawa mai nama kusa da kofar shiga gidan zoo ta biyu.
Allah mai zamani yanzu Zoo Road ta zama ɗaya daga cikin manyan titunan da ake ji dasu a Kano a ɓangaren Kasuwanci.
June 12 1993. An yi tashin hankali an kashe hausawa da yawa a Legos da sauran yankunan yarbawa. A nan Arewa ma an Kashe ƙabilu da dama sbd lokacin ba a banbance Yarbawa da Inyamurai da sauran ƙabilu. Kawai in kai ba Bahaushe bane duk kuɗin goro ake musu.
June 12 1993. Itace ranar da babangida ya soke zaɓen da ake Kyautata zaton Abiola ne ya lashe zaɓen duk da ba a kai ga bayyana sakamakon zaɓen ba. Amma a yadda alƙaluma suka nuna shine kan gaba akan abokin karawarsa wato marigayi Alhaji Bashir Usman Tofa.
Allah ya gafarta musu baki ɗaya. Ya kyautata namu zuwan.
Shi Kuma Babangida da ya rage a raye, Allah ya rabashi da duniya lafiya.
Lokacin muna makaranta ni da wasu abokaina mun ɗauki sarar June 12 idan ana magana muka ce June 12, muna nufin tashin hankali kenan .
Allah ya zaunar da ƙasar mu Nijeriya lafiya. Ya kawo mana shugabani nagari. Waɗanda ƙasar ce a gabansu ba wai tara kuɗi da zalunci ba.
Rubutawa :- Abdullahi Jibril Ɗankantoma
UNCLE LARABI
Abdullahi Jibril Larabi
KANO State. Nigeria
08065418892.
