
Daga BELLO A. BABAJI
Masanin shari’a kuma babban lauya a Nijeriya (SAN), Sunusi Musa, ya ƙalubalanci matakan da aka bi wajen bada kyautar karramawa ta ƙasa da aka gudanar a yau Ranar Dimukraɗiyya.
Ya ce, an yasar da wasu da suka yi gwagwarmayar kafa mulkin dimokraɗiyya tun daga zaɓen Shugaban Ƙasa da aka soke na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.
A wani saƙo da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook, Babban Lauyan ya hasato wasu mutane da ya ke ganin ya kamata a ce suna daga cikin waɗanda aka karrama, amma rashin jin sunayensu ya sa ya bayyana jaddawalin waɗanda aka karrama a matsayin abinda bai cika ba.
Ya kuma ce, duk da cewa akwai sunayen Yar’Adua da Gambo Sawaba a ciki duba da gudumawarsu ga zaɓen June 12, to lallai Abubakar Rimi da Sule Lamiɗo da Tony Anenih da Kanal Ɗangiwa Umar da kuma Atiku Abubakar sun cancanci a sanya sunayensu daga ciki.
Shugaba Bola Tinubu ya karrama mutane 65 waɗanda ke raye da kuma matattu, inda ya ce hakan ya samu ne saboda gudumawa da hidima da suka yi wa Nijeriya da al’ummarta.
Daga cikinsu akwai Wole Soyinka, Femi Falana (SAN), da marigayiya Kudirat Abiola, wadda aka karrama da Kwamandar Jamhuriyar Tarayya (CFR).
Sauran sun haɗa da marigayi ɗan jarida Bagauda Kaltho, Shehu Musa Yar’Adua (GCFR), Dakta Beko Ransome-Kuti (CON), da tsohon gwamna Balarabe Musa (CFR) da dai sauransu.
