Daga USMAN KAROFI
C&C Friends Foundation ta taya al’ummar Najeriya murnar zagayowar Ranar Dimukuraɗiyya ta bana, tana mai bayyana ranar a matsayin lokaci na tunani, murnar nasarori da kuma sabunta ƙudurin ci gaba da kare dimokuraɗiyya a ƙasar.
A cikin saƙon taya murnar da shugaban ƙungiyar na ƙasa, S. G. Kalambaina, ya fitar, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da nuna kishin ƙasa da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.
“Yuni 12 rana ce da ke tunatar da mu muhimmancin dimokuraɗiyya da irin ci gaban da Najeriya ta samu a wannan tafiya,” in ji Kalambaina. “Mun yi imani cewa wannan biki zai ci gaba da ƙarfafa dunƙulalliyar kasa da haɗin kai, domin samun ci gaba mai ɗorewa.”
Ƙungiyar ta kuma yi fatan alheri da zaman lafiya ga kowa da kowa a fadin Najeriya, tana roƙon Allah ya cigaba da albarkata ƙasar da shugabanninta.
