‘Yan sandan Katsina sun ceto mutane 73 da aka yi garkuwa da su

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta sanar da kuɓutar da wasu mutane 73 daga hannun masu garkuwa da mutane tare da cafke sama da mutane 175 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a yayin gudanar da aikin tsaro cikin watan Mayun 2025.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan nasarorin da rundunar ‘yan sandan ta samu cikin watan da ya gabata.

A cewar DSP Sadiq, waɗanda aka kama sun haɗa da mutane 15 da ake zargi da aikata laifin fashi da makami, 20 da ake zargi da aikata laifin kisa ko kuma kisan kai, da kuma wani mutum da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da mutane.

Bugu da ƙari, an kama mutum ɗaya da mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba, yayin da aka kama mutane 30 da ake zargi da aikata laifukan fyaɗe. An kuma kama wasu mutane 108 bisa wasu laifuka na daban.

Abubuwan da rundunar ta ƙwace sun haɗa da:

Bindigar AK-49 da aka ƙera gida da bindigar revolver ita ma ƙirar gida da kuma harsashi 506 mai girman 7.62mm. Rundunar ta kuma samu nasarar ƙwato babura bakwai da ake zargin an sace su, sai kuma dabbobi 174 da ake zargin na sata ne.

DSP Sadiq ya alaƙanta wannan nasarar da rundunar ta samu bisa ga goyon bayan da rundunar ke samu daga gwamnatin jihar Katsina da kuma haɗin kan da al’ummar ke bayarwa.

By ukarofi