Ranar Dimukraɗiyya: Buni ya ayyana al’ummar Yobe a matsayin ginshiƙin Dimukraɗiyya

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba bisa goyon bayan da al’ummar jihar suke baiwa manufofi da ingantattun tsare-tsaren gwamnatinsa, inda ya bayyana su a matsayin ginshikin dimokuraɗiyya.

A cikin sanarwar Ranar Dimukraɗiyya, wanda Mamman Mohammad, mai magana da yawun Gwamna Buni ya sanyawa hannu, ya bayyana al’ummar jihar a matsayin ƙashin bayan mulkin dimokraɗiyya a Yobe.

Ya ce shekaru 26 da ɗorewar mulkin dimokraɗiyya a Nijeriya, wanda ya baiwa yan ƙasa damar zaɓar shugabani don su mulke su.

“Ta hanyar Dimukraɗiyya ce al’ummar mu suke bayyana ra’ayoyin su, tare da cikakkiyar damar tsunduma cikin harkokin mulki da tsara manufofi.” In ji Buni.

Gwamnan ya bayar da misali dangane da shigar matasa a harkokin gwamnatinsa, inda ya naɗa matasa a muƙamai daban-daban, wanda ya haɗa da kwamishinoni, shugabannin ma’aikatu, masu bayar da shawara, da wakilai a matsayin wani yunƙurin inganta gwamnati.

“A Yobe, muna da manufar buɗe ƙofofin mu don tabbatar da cewa al’ummar jihar suna bayar da gudummawa mai ma’ana kan harkokin gwamnati, kuma a dama dasu.” In ji shi.

Buni ya nuna kyakkyawan fata game da makomar jihar, inda ya bayyana shigar matasa cikin siyasa a matsayin ci gaban dimukraɗiyya.

Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa za a sami ƙarin ribar dimokuradiyya, kuma ya yi alkawarin kammala ayyukan da suke gudana don amfanin jama’a.

Gwamnan ya yi kira ga jama’ar jihar su yi amfani da lokacin damina don yin aikin noma, kuma su ci gaba da baiwa hukumomin tsaro goyon baya, don samun haɓaka zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

By ukarofi