Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mazauna wasu yankunan da dama a jihohin Zamfara da Neja sun sake shiga wani mawuyacin hali, bayan da sanannen jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji, ya buƙaci a biya naira miliyan 50 kafin a basu damar fara aikin noma na bana.
Manhaja ta rawaito cewa wannan buƙatar ta fito fili ne ta bakin wani mai nazarin tsaro mai suna Bakatsine, wanda ya wallafa bayani a shafinsa na ɗ , inda ya bayyana cewa shugaban ‘yan bindigar ya ƙaƙaba kuɗin a matsayin sharaɗi na samun zaman lafiya.
A cewarsa, “An bada rahoton cewa shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, yana buƙatar naira miliyan 50 daga mazauna Tsalaken Gulbi daga kauyen Fakai, Karamar Hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara, har zuwa ƙaya da ke kusa da iyakar Jihar Neja, kafin ya barsu su yi noma a kakar bana,” inji Bakatsine.
Bello Turji na daga cikin fitattun shugabannin ‘yan bindiga da aka dade ana danganta su da hare-hare masu muni, garkuwa da mutane da kuma haramtaccen karbar haraji daga kauyuka.
Rahotanni sun ce ikon Turji ya mamaye wasu sassa na jihohin Zamfara, Sakkwato da Katsina.
